23 Yuli 2019 - 04:34
‘Yan Adawa A Sudan Na Tattaunawa A Habasha

‘Yan adawa da kungiyoyin farar hula da na masu dauke da makamai a Sudan a daya bangare, sun fara wata tattaunawa yau Lahadi, a birnin Adis-Ababa na kasar Habasha, domin magance sabanin dake tsakaninsu, bayan cimma yarjejeniya da sojojin dake rike da mulki a kasar ta Sudan.

(ABNA24.com) ‘Yan adawa da kungiyoyin farar hula da na masu dauke da makamai a Sudan a daya bangare, sun fara wata tattaunawa yau Lahadi, a birnin Adis-Ababa na kasar Habasha, domin magance sabanin dake tsakaninsu, bayan cimma yarjejeniya da sojojin dake rike da mulki a kasar ta Sudan.

Tattaunawar na hada wakilan kawacen samar da ‘yanci da sauyi na kasar da ya kunshi kungiyoyin fara hula da jam’iyyun adawa da kuma wakilan gungun masu dauke da makamai na yankin Darfur.

Da yake karin bayyani ga manema labarai, Rabeh Mahdi, na kawacen samar da ‘yanci da sauyi an Sudan, ya ce, dole ne a magance sabanin dake akwai tsakanin bangarorin, saboda har yanzu ba’a tattauna mahimman batutuwa ba.

Amma wasu daga cikin mahimman batutuwa da yace wasu na son a tattauna akansu, sun hada da samar da batun zaman lafiya, wanda suke so a saka a cikin yarjejeniyar da aka cimma da sojoji a kwanakin baya, da kuma kafa gwamnati.

Saidai wasu mambobi na kawancen basu amince da shawarar ba, inda kawai suke bukatar a kafa gwamnati kawai a cikin lokacin da ya tsawaka.




/129